Labarai | 23.01.2008 | 07:00 UTC
Dubban mazauna a Zirin Gaza sun kwarara cikin Masar
Dubun dubatan Palasɗinawa daga Zirin Gaza sun kwarara zuwa cikin Masar bayan an fasa ramuka da dama a cikin bangon da ya raba iyakokin Gaza da Masar. Mutane sun yi ta rige-rigen sayen abinci, mai da dai sauran kayakin masarufi da suka yi ƙaranci sakamakon toshe kan iyakokin Gaza da Isra´ila ta yi. Masu tsaron kan iyakokin Masar ba su ɗauki wani mataki ba lokacin da ´yan Gazan ke kwarara suna tsallake kan iyakar. ´Yan sanda daga Gaza dake ƙarƙashin ikon Hamas su ma sun tsaya ne suna kallon abbubuwan dake wakana. Bayan kwanaki biyar da rufe dukkan hanyoyin dake shiga Gaza a jiya talata Isra´ila ta kyale an shiga da gas na girki da kuma mai ga tashar samar da wutar lantarki guda daya tilo a Gaza. Tun a ranar lahadi aka rufe tashar saboda ƙarancin mai. A kuma halin da ake ciki kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani taron gaggawa inda ya tattauna akan rikicin dake ƙara yin tsamari a Gaza.
More briefs
Annan ya fara yin sulhu a rikicin siyasar Kenya | 23.01.2008
´Yan sanda sun awon gaba da jagoran ´yan adawa a Zimbabwe | 23.01.2008
Hare-haren Isra´ila a Zirin Gaza barazana ce ga zaman lafiya | 19.01.2008
Tashe-tashen hankula a Iraqi a ranar bukin Ashura | 19.01.2008
An sako Turawan nan uku da aka tsaresu a Kenya | 19.01.2008
´Yan sandan Pakistan sun cafke wani matashi bisa zargi kisan Bhutto | 19.01.2008
Shugaba Abbas ya baiyana matakin sojin Isra´ila a Gaza da cewa kisan kare dangi ne | 16.01.2008
Wani hari a Sri Lanka ya halaka mutane da yawa | 16.01.2008







