Duniyar ɗan Adam | 25.05.2008
Afrika ta cigaba a shekara ta 2007 inji rahoton OECD
Tattalin arzikin Afirka ya bunkasa a shekara ta 2007 inji rahoton sheklara na OECD
A wannan karo shirin zai duba rahoton da hukumar haɗin kan tattalin arziki da raya ƙasa, wato OECD ta bayyana, a game da cigaban da Afirka ta samu a shekara ta 2007, da kuma ƙalubalen dake gaban wannan nahiya ta fannin kyauttata rayuwar jama´arta.
Rahoton na Hukumar OECD, tare da haɗin gwiwar babbar bakin raya ƙasashen Afirka ya gudana cikin ƙasashe 35.
A wani saban yunƙuri na tada komaɗar tattalin arziki, binciken da hukumar ta gudanar, ya gano cewar a bana ma, Afirka tayi abun azo a gani ta fannin cigaba.
Tun tsukin shekarau huɗu da suka wuce, al´ammura sun fara cenzawa a cikin ƙasashe da dama, ta hanyar yunƙurar tattalin arziki.
A shekara bara, ci gaba da Afirka ta samu ya kai 5,7 cikin ɗari idan aka kwantanta da shekara ta 2006.
Sannan abun alfahari, wannan bunƙasa zata dawwama hatta a shekara da muke ciki ta 2008, ta kuma ƙara haskaka a shekara ta 2009, kamar yadda Helmut Reisen shugaban cibiyar bincike na OECD ya bayyana.
Wani abun da ke taimakawa Afrika ta samu wannan ci gaba shine bunƙasar zuba jari.
Ƙasashe kamar su China, Indiya, Russia, da kuma Brazil, sun zuba jari babu ƙaƙƙabtawa a nahiyar Afirka.
To saidai wannan ci gaba ya fi tasiri a ƙasashen da suka mallaki albarkatun man fetur, ta la´akari da tashin gwabran zabo da wannan makashi yayi a kasuwanin duniya.
Sannan a tsakanin ƙasashen masu man petur, cigaban ya bambamta daga wannan ƙasa zuwa wacen.
Ƙididigar ta nunar da cewar, Equatoriale Guine, Lybia da Angola suke sahun gaba.
Suma ƙasashen Afirka, wanda basu mallaki man petur ba , amma suka yi suna wajen sayar da ƙarafa,da albarkatun noma a ƙasashen ƙetare, sunci babbar gajiya a dalili da tsadar farashen kayan abinci.
daga rukunin wannan ƙasashe, akwai Mozambique Namibiya, Afrika ta Kudu da Zambiya.
A jimilce, 12 daga sahun ƙasashe 35 da binciken ya shafa, sun ƙara yawan hajojin da suke saidawa ƙetare da kashi biyar cikin ɗari.
Shugaban babbar bankin raya ƙasashn Afirka, Donald Kaberuka ya yaba matuƙa, wannan cigaba da Afirka ta samu, saidai yace ,ya zama wajibi ya zama dawwammame, ya kuma shafi dukkan ƙasashen nahiyar.
A game da haka, matakin da ya cencenta a ɗauka shine tallafawa harakokin noma wanda shine tushen arziki, ya kuma cigaba da cewa:a tsawan dogon lokaci, harakokin noma a Afrika sun fuskanci matsaloli ta fannoni dabam -dabam, hasali ma rashin darajar kasuwar albarkartun noma, tsadar takin zamani, ƙarancin hanyoyin zirga zirga, sai kuma shinge cinikayya da ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki ke gindayawa albarkatun noman Afirka.
Idan aka magance wannan matsaloli, ko shakka babu, Afirka za ta ba maraɗa kunya ta fannin bunƙasar tattalin arziki.
Babbar bankin raya ƙasashen Afrika, a zaman taron da ta shirya cikin wannan wata a birnin Maputo na Mozambique, ta yanke shawara ware magudan kuɗaɗe domin sayen takin zamani da gwamnatocin Afirka za su rabawa manoman su.














