Duniyar ɗan Adam | 08.05.2008
Ölpreis
Man Fetur yayi tashin gwabran zabo. Ganga ɗaya ta kai dalla 123.
Farashen man petur na cigaba da tashin gwabran zabi a kasuwanin duniya, inda a yanzu ganga ɗaya ta kai dalla Amurika 123.
Wannan shine karon farko da gangar ɗayan mai ɗaya , wato lita 159,ta kai dalla123 a cikin tarihin hada hadar makamashi ta duniya.
Tunda jimawa, masana a game da kasuwar man petur suka yi hasashen wannan tsada, wadda a cewar su ganga ɗaya na iya kaiwa ga dalla 200, muddun ba a ɗauki matakan da suka dace ba tun da sauran wuri, kamar yadda David Wyss na kamfanin cinikin makamashi mai suna Rating Standar Poors ya nunar:
ya ce mun jima muna sa ido a game da tafiyar farashen kuma cemma mun san a rina.
Tun shekaru shida baya, farashen ya fara yin sama inda sannu a hankali ya kai dalla 100.
A shekara ta 2002 an sayi gangar ɗanyan mai ɗaya tsakanin dalla 19 zuwa 21.
A shekarun gwammai na 1980 ,an fuskanci man petur, wadda ta sa farashe ya ƙaru da kashi 8 cikin ɗari.
Saidai bambanci da na wannan karo shine cewar tsadar man na wakana a daidai lokacin da Amurika ke fama da kariyar tattalin arziki da kuma tazara da Euro ke cigaba da baiwa dalla Amurika,wadda da ita ne ake gudanar da dukan cinikayar da ta shafi man petur a manyan kasuwanin duniya.
Wannan matsaloli biyu sun jawo illoli masu yawa ga tattalin arzikin sauran ƙasashen duniya, inji Anthony Grisanti na kamfanin GRC-Energy: kamar mahaukaciyar guguwar Hurricane, matsalar kariyar tattalin arzikin Amurika ta bazu a duniya.
Rikicin da ya ke wakana a yankin gabas ta tsakiya ya kuma ƙara hauda wannan farashi.
Bayan rikicin na gabas ta tsakiya mussamman ma takon saƙon da aka shiga tsakanin Iran da ƙasashen Turai da Amurika, dillalan man petur sun dangata wannan mumunar tsadar mai da tashe tashen hankula a yankin Niger Delta dake Tarayya Nigeria, inda Ƙungiyar MEND ke ci gaba da kai hare hare ga bututun mai na kamfanonin dake haƙar man petur a wannan yanki.
A nata gefe, Ƙungiyar ƙasashe masu albarkatun man petur warto OPEC ta ce ba za ta ƙara yawan ma da take haƙƙowa ba, dauzkar wannan mataki bisa dukan alamu zai ƙara tada hankulla da rudamin fuskantar wani yanayi ,inda amfani da man petur zai gagara mai ɗan ƙaramin ƙarfi.
Ƙungiyoyindsake fafatakar kare mahhali sun nunar da cewa Hanya ɗaya tilo ta kawo ƙarshen matsalar, ita ce ta yawaita amfani da makashi ta hanyar sarafa hasken rana, tsirai da kuma iska.












