Duniyar ɗan Adam | 02.06.2008
Ticad Konferenz
Sakamakon taron tattalin arziki da ya haɗa tawagogin Afirka da na Japan a Yokohama.
A ƙarshen watan Mayu na shekara ta 2008 ne tawagogin Afrika da na Japan suka shirya wani mahimmin taro da aka fi sani da suna Ticad, wanda ke gudanar da bita da kuma tsara mu´amilar cinikayar diplomatia da ta siyasa, tsakanin nahiyar Afirka da Japan.
A wannan karo, an shirya taron a birnin Yokohama kussa da Tokyo, ya kuma samu halartar shugabanin ƙasashen Afirka ko na gwamnatoci fiye da arba´in.
A wannan karo, shirin ciniki da masana´antu, zai duba irin sakamakon da taron ya cimma.
Daga ranar 27 zuwa 30 ga watan Mayu na wannan shekara aka shirya taro tsakanin ƙasashen Afirka da Japan.
A tsawan kwanaki huɗu, tawagogin biyu sun tattana mahimman batutuwa da suka shafi mu´amilar saye da sayarwa, da taimakon raya ƙasa, domin taimakawa Afirka ta fita daga matsalar talauci.
Ƙungiyar Tarayya Afirka, ta bayyana gamsuwa ga sakamakon taron da ya haɗa Afirka da Japon a birnin Yokohama.
Shugaban ƙasar Tanzaniya, Jakaya Kikwete, bugu da ƙari shugaban Ƙungiyar AU, ya bayyana hakan a jawabinsa na rufe taron.
Bayan mahaurorin na tsawan kwanaki ukku da ɓangarorin biyu suka tafka, Japan ta alƙwarata tallafawa Afirka bil haƙi da gaskiya wajen yaƙi talauci.
A game da haka sun bayyana wani tsari na mussamman ta fannin bunƙasa harakokin noma kamar yadda Firaministan Japan Yasua Fakuda ya nunar, tare da cewa:
Tsakanin Japan da Afrika, mun buɗa wani saban babe na tarihi mai suna ƙarnin Afrika.A game da haka, za mu lunka taimakon raya ƙasa da muke baiwa wannan nahiya daga nan zuwa shekara ta 2012.
A cikin yarjejeniyar da aka cimma,ƙasashen Afirka ,sun yi na´am da ƙara yawan cimakar da suke nomawa da kashi 6% ,nan da shekara ta 2015, ta hanyar ware kashi 10 cikin ɗari na kuɗaɗen da suka mallaka domin inganta noma.
A nasu gefe, hukumomin Tokyo, sun bayyana gama ƙarfi da Afirka, wajen bunƙasa noman shinkafa nan da shekaru 10 masu zuwa kamar yada muinistan harakokin wajen ƙasar ya nunar:Japan zata taimakawa Afrika ta fannin noman shinkafa, ta yadda zata ƙara yawan shinkafar da take nomawa ta Tan miliyan 14 nan da shekaru goma masu zuwa.
Don cimma wannan buri, Afrika da Japan sun rattaba hannu akan yarjejeniya domin ƙara filayen noman shinkafa da kashi 20 cikin ɗari.
A wani ɓangaren kuma, mahalarta taron Yokohama, sun bayyana gamsuwa a game da kwanciyar hankalin da ta fara wanzuwa a mafi yawan ƙasashen Afirka da suka yi fama da yaƙe- yaƙe.
A game da batun lafiya, Japon ta ambata taimakawa Afrika wajen yaƙi da cuttutukan da suka zama gagarabadau, mussamman tarin fuka.
Shugaban bankin Duniya Robert Zoelich na ɗaya daga shugabanin kafofin taimako na duniya da suka halarci taron Yokohama,ya alƙawartawa shugabanin ƙasashen Afirka ko na gwamnatoci fiye da 40 da suka halaraci wannan taro, cewar zai iya ƙoƙarinsa, domin ciwo kan ƙasashe masu hannu da shuni su taimakawa Afrika: muna buƙatar cigaba, daga bayyanai na fatar baka, zuwa ayyuka na zahiri.
Yauni ya rataya kan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki, suyi tattanawa ta zahiri a zaman taron G8 mai zuwa.
A birnin Tokyo na ƙasar Japan ne, Ƙungiyar G8 zata wannan zaman taro a watan Juni na wannan shekara, a game da haka shima Firaminista Yasuo Fukuda, ya bayyana aniyarsa, ta yin amfani da damar, domin tattanawa da takwarorinsa na G8 a kan wajibcin tallafawa Afirka.
Saidai a yayin da yake bayyani ,shugaban ƙasar Afirka ta Kudu Tabon Mbeki ya ce Afirka ta fi buƙatar daidaita harakokin cinikayya da sauran sassa na duniya a maimakon taimakon raya ƙasa:mussamman ta kamata mu fahinci cewar, tallafawa Afirka ta fannin harakokin kasuwa ya fi tasiri akan basu taimakon raya ƙasa.
Muddun ba a daidaita sahun mu´amilar saye da sayarwa ba, taimakon raya ƙasa ba zai taka rawar gani ba, wajen wanke dauɗar talaucin Afirka.
A game da taimakon raya ƙasa, Japan tayi alƙawarin lunka kuɗin da take ba Afirka, daga Euro miliyan 580 zuwa Euro miliyan dubu ɗaya da ´yan ka ko wace shekara.
A game da bunƙasa harakokin cinikaya Japan ta gayyaci kamfanoni da masana´antu su zuba jari a Afirka , domin gwamnati ta tanadi tsari na mussamman wanda zai tallafa dukan kamfanoni da masana´antu Japan ta fannin ƙarfafa mu´amilar cinikayya da Afirka.
Hukumomin Tokiyo sun bayyana aniyar ƙara kutsawa a nahiyar Afirka kamar sauran ƙasashe masu tasowa a duniya wanda suka haɗa da China da Indiya, wanda tarmamuwarsu ke haskawa yanzu a Afirka.











