1. main content
  2. main navigation
  3. extra content
  4. head navigation
  5. search
  6. Choose form 30 Languages


 

Duniyar ɗan Adam | 07.06.2008

Taron cigaban tattalin arzikin Afirka

An kammalla taron cigaban tattalin arzikin Afirka a birnin Cap Town na Afirka ta kudu



Daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Juni ne tawagogi daga ƙasashe dabam dabam na duniya, suka halarci taron ƙasa da ƙasa, a game da haɓɓaka tattalin arzikin Afrika.

Wannan taro ya gudana  a birnin Cap town na Afrika ta Kudu.

Mahalarta a ƙalla 850 wanda suka haɗa da ´yan siyasa da shugabanin kamfanoni da masana´antu daga ƙasashe fiye da 50 suka tabka mahaurori, a game da hanyoyin  bunƙasa tattalin arzikin Afirka.

Daga mahalarta taron akwai shugaban Tarayya Nigeria, Al Haji Umaru Musa Ya Adua, da shugaban ƙasar Burundi Pierre Nkurunziza, da takrawansa na Ghana John Kuffor, da dai sauran tawagogi dabam dabam.

Mahalarta taron Cap Town sunyi amfani da wannan dama, domin feɗe biri har ga wutsiya, a game da illolin dake hana ruwa gudu ta fannin ci gaban Afrika, kazalika, sun gabatar da shawarwari wanda za su kasance madogara ga ƙasashen Afrika don ƙara bunƙasar cigaba.

Taron na bana, ya wakana  a daidai lokacin da babbar bankin Afirka ta bayyana rahoto da ya nunar da cewa, a shekara bana Afirka ta samu cigaba da kashi fiye da biyar cikin ɗari.

Shugaban ƙasar Afrika ta kudu mai masaukin baƙi yace wannan hoɓa sarma da Afrika ta shiga zai ɗorewa:

Wannan hoɓa sarma da Afrika tayi ta fannin cigaba, babu gudu babu ja da baya.

Duk da cewar cigaba ne wanda ya bambanta daga wannan ƙasa zuwa wacen, amma a jimilce na yi imanin cewar Afirka ta yunƙura kuma babu sauran ja da baya.

Jama´a na bayyana ra´ayoyi iri-iri a game da matsalolin dake tauye cigaban Afrika, wasu na ambata makircin turawan mulkin mallaka, to saidai a cewar saban Firaministan ƙasar Kenya Raila Odinga, rashin sannin makamar aiki, da cin hanci,da wasu shugabanin Afirka suka shahara akai, sune suka dabaibaye Nahiyar, a saboda haka, kar Afirkawa suyi kuka da turawan mulkin mallaka.

Sha´anin tsaro na taka muhimmiyar rawa wajen nakasa Afirka, domin ƙasashe da dama na fuskantar yaƙe- yaƙe, au a cikin gida, ko kuma da ƙasashe maƙwabta, saboda haka, shugaban ƙasar Burundi Pierre Nkurunziza, wanda ƙasarsa ke fama da rikicin tawaye, ya gargaɗi Afirkawa su himmantu wajen samar da zaman lafiya, muddun suna da burin samun ci gaban wannan nahiya.

A dangane da rashin matakan tsaro kyakyyawa da dama daga kamfanoni da masana´atu na ƙetare ke shakkun zuba jari  a Nahiyar Afrika, to saidai a cewar Sultan Ahmed bin Suleiman, shugaban rukunin wani kamfanin zuba jari daga Daular Larabawa, mai suna Dubai World, bai kamata a dangata zuba jari da batun tsaro ba a Afirka:

Kamar sauran kamfanoni na duniya, muma, mun yi ta jin jita-jitar dake cewar akwai matuƙar haɗari mutum ya zuba jari  a Afrika, to saidai a zahiri wannan ruɗu ne kawai, da ya riga ya shiga zukatan mutane.

Abunda ke tabbas shine: Afrika ta kama turbar cigaba, kuma muna fata kamfanoni da masana´antu na duniya suyi koyi da mu ,wajen zuba jari a wannan nahiya, domin akwai riba matuƙa.

Babu shakka an samu lafawar ƙura a mafi yawan yankunan dake fama da tashe tashen hankulla  a Afrika, to saidai har yanzu da sauran rina kaba.

Ƙasashen dake rayuwa a yanayin zaman lafiya, sun fi sauran samun cigaba , ta wannan fanni ƙasar Ghana na daga jerin ƙasashen Afrika da ake bada misali ,ta la´kari da cigaba da take samu babu ƙaƙƙabtawa, kamar yadda shugaba John Kuffor ya bayyana a yayin da yake jawabi gaban mahalarta taron.

Bayan mahaurori na yini ukku, mahalrata taron Cap Town, sun gabtar da shawarwari wanda za su taimaka wajen dawwamar cigaba da Afrika ta fara samu.

Shawarwarin sun haɗa da ƙara ƙarfafa mua´mila da cuɗe ni in cuɗe ka, tsakanin ƙasashen Afrika, kamar yadda shugaban Tarayya Nigeria Al Haji Umaru Musa Yar Adua yayi bayyani.

Shi kuwa shugaba Mutharika na Malawi, kira yayi da a ƙara maida himma ga harkokin noma ,domin shine tushen warke talaucin da Afrika ke fama da shi:

Duniya na fuskantar ƙaracin abinci kamar yadda muka shaida a Afrika.

Nahiyar Afirka na iya taka rawar gani wajen magance wannan matsala, saboda filayen noma da muka mallaka, wannan kuma hanya ce ta ƙara bunƙasa tattalin arziki.

A halin da ake ciki dai ƙiddidigar da masana harakokin tattalin arziki suka gudanar, ta gano cewar fiye da kashi 40 cikin 100 na al´ummar Afrika, kussan miliyan dubu ɗaya ke fama da matsananci talauci, wanda kuma har yanzu basu gani ba a ƙass cigaba da ake shelar Afirka ta samu.

Saboda haka yauni ya rataya  akan hukumomin ƙasashe dabam dabam na Afirka  su ƙara maida himma don cimma burin da aka sa gaba da wanke ɗaudar talauci da yayi ƙwai ya ƙyenƙyashe a bainin jama´a.

Sanarwar ƙarshen taron ta ɗorawa ƙasar Kenya yaunin shirya haɗuwa ta gaba  a shekara ta 2010.

 

Yahouza, Sadissou

 
Share this article

Send us an e-mailSendPrint

More on the topic



 
Picture of the Day
ImageOfTheDay

DW-TV EUROPE live

Journal (english) - With In Depth