Duniyar ɗan Adam | 07.07.2008
G8 Afrika
Taron shugabanin ƙasashen G8 a Japan, ya tattana a game da matsalaloin ɗumamar yanayi, tsadar makamashi, da ta abinci, da kuma taimakon raya ƙasa
A wannan karo shirin zai je da mu ƙasar Japan, inda shugabanin ƙasashen G8 suka shirya taron ƙoli na shekara shekara daga 07 zuwa 08 ga watan juli na shekara ta 2008.
Taron ya tattana batutuwa dabam dabam wanda suka haɗa da taimakon raya ƙasa da G8 ke baiwa Nahiyar Afrika.
A cikin shirin na wannan lokaci, za mu duba sakamakon taron, mussamman a game da Afrika da kuma sukar da ƙungiyoyin fara hulla suke yiwa mu´amila tsakanin G8 da Afrika.
Daga ranar 07 zuwa 08 ga watan da muke ciki shugabanin ƙasashe 8 mafi ƙarfin tattalin arziki a duniya, da aka fi sani da suna G8,wato Jamus France, Italiya, Britaniya, Russia Kanada, da Amurika, suka shirya zaman taron ƙoli na shekara shekara, a birnin Hokaido na ƙasar Japan.
Kamar yadda suka saba, sun tattana batutuwa dabam dabam, da suka jiɓancin siyasa, cinikayya da sauran mu´amila a tsakaninsu.
A wannan karo, shugabanin G8 sun gayyatao takwarorinsu bakwai daga Afrika, wato shugabanin ƙasashen Algeria,Afrika ta Kudu, Ethiopiya Ghana, Senegal, Tanzaniya da Tarayya Nigeria.
An ware ranar farko domin ganawa ta ƙeƙe da ƙeƙe, tsakanin masu faɗa aji na duniya da wakilan Afrika.
Shugabanin Afrika sunyi amfani da wannan dama, inda ido da ido suka bayyanawa shugagabninG8 cewar sungaji da gafara sa ba su ga kafo ba,wato sungaji da alkawura nafatar baki ba tare da cikawa ba.
Idan ba a manta ba , abarkacin taron da ya wakana a Gleaneagles,a shekara ta 2005, G8 ta alƙawarata lunka taimakaon raya ƙasar da take baiwa Afrika, har zuwa shekara ta 2010, domin taimakawa nahiyar mafi talauci aduniya, ta cimma burin rage raɗaɗin ƙuncin rayuwa, kamin nan da shekara ta 2015, a ƙarƙashin tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya na Millenium Developpment Goals.
To saidai a cewar tawagar Afrika ya zuwa yanzu ba a samu kashi 20 cikin ɗari ba, na wannan alƙawari.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel dake halartar taron, tace lalle G8 na da babban yauni a kanta, wanda kuma ya zama wajibi ta sauke.
A ɗaya wajen Merkel ta nuna illolin dake tattare da tallafin da ƙasashen G8 ke baiwa manomansu ta fannin hauhawar farashen abinci da duniya ke fama da shi.
Sannan ta ambata wani saban alƙawari da Ƙungiyar Tarayya Turai da kuma Jamus suka yi wa Afrika don farfaɗo da ayyukan noma.
" An samu alƙawura bada taimako masu yawa.
Hukumar zartaswa ta Ƙungiyar Tarayya Turai tace za ta taimaka cikin gaggawa da Euro miliyan dubu ɗaya, a yayin da ƙasar Jamus zata bada taimakon Euro miliyan ɗari shida, don farfaɗo da ayyukan noma a wannan shekara a nahiyar Afrika,ta la´kari da matsalolin abinci da duniya ke fuskanta, ya fi dacewa mu bada fifiko ga ayyukan noma a manufofinmu na taimakon raya ƙasa".
A lokacin da yayi nasa bayyani, Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon, yace bai kamata ba, a ci gaba da ɗaukar sabin alƙawura ba tare da an cika wanda suka gabata ba, a game da haka, yayi kira da babbar murya, ga shugabanin ƙasashen G8 su baiwa Afrika kuɗaɗen da suka ambata tun farko.
Ƙungiyoyin fara hulla a ko wace shekara na shirya nasu taron domin ƙalubalantar taron G8.
A wannan karo wakilai daga sassa dabam dabam na Afrika, sun haɗu a birnin Katibugu dake tazara kilomitia 100 da Bamako babban birnin ƙasar Mali, domin masanyar ra´ayoyi a taron da suka raɗawa suna mambarin talakawa.
Madame Bari Aminata Ture, itace shugabar haɗin gwiwar Ƙungiyoyin ƙasar Mali masu adawa da G8, ta kuma yi ƙarin haske a game da bambanci tsakanin taron G8 da na mumbarin talakawa.
" Su suna mahaurori ne a game da matsalolin ɗumumar yanayi, a yayin da mu a ganinmu, tushen ɗumamar yanayin shine wassoson da suke yi da dukiyar ƙasashe masu tasowa, saboda haka suna yawo ne kawai da hankulan jama´a.
A namu taron, muna gayyato wakilan ainahi na talakawa, domin tattanawa a game da matsaloli na zahiri da suke ci masu tuwo a ƙwarya."
A shekaru biyu da suka wuce, Jamhuriya Niger ta karɓi baƙunci taron mumbarin talakawa, wanda ya samu halartar wakilai daga sassa dabam dabam na ƙasar da ƙasashe waje.
Musa Tchangari shine ya jagoranci wannan taro, na kuma gayyato a cikin shirin, inda ya bayyana dalilan da suka sa Ƙungiyoyin fara hulla yin adawa da taron G8.
Ƙungiyoyin fara hulla sun yi Allah wadai da mu´amila kashin dankali inda manya ke tausne ƙanana tsaknain G8 da ƙasashe masu tasowa, don daidata sahun al´ammuran sun bada shawarai.











