Duniyar ɗan Adam | 15.07.2008
Fraport
Filin saukar jiragen sama na Frankfort da mu´amilarsa da ƙetare.
A wannan karo zai kai mu filin saukar jiragen sama na birnin Frankfort a nan ƙasar Jamus, inda na wakilici sashen hausa a cikin wata tawaga ta ta kai ziyara gani da ido a wannan filin jirgin.
Filin saukar jiragen sama na birnin Frankfort da aka fi sani da suna Fraport ya fara aiki tun shekara ta 1924 , kuma shine mafi girma a nan ƙasar Jamus, kazalika, yana daga cikin filayen saukar jiragen sama da suka yi suna suka fi kuma girma a duniya.
Fraport na da ma´aiakata dubu 70, wanda ke aiki a sassa dabam dabam.
Ya na gudanar da ayyuka tare da haɗin gwiwa da wasu manyan kamfanoni na Jamus wanda suka haɗa da kamfanin jirage na Lufthanza, da Julius Bär,Hesse, taubon Hodson, da dai sauran su.
A shekara da ta gabata, Fraport ya samu ribar da yawanta ya kai Euro miliyan dubu biyu da ´yan ka.
A ko wace awa ɗaya, akawi jirage a ƙalla 200 dake sauka kokuma suke tashi daga Fraport, a ko wace rana,Fraport na jigilar passenjoji kimanin dubu 150.
Kamfanoni jiragen sama 125 ke amfani da wannan filin jirgi, domin jigillar mutanen,kokuma kaya zuwa filayen jiragen sama fiye da 300 a ko ina cikin duniya.
To saidai a halin da ake ciki, Fraport kamar sauran filayen jiragen sama na cikin halin zullumi na raguwar hada hada ta la´akari da tsadar man petur a kasuwanin duniya.
Wata ƙididiga da Ƙungiyar filayen jiragen samar ta ƙasa da ƙasa ta gudanar, ta gano cewar a tsawan watani 12 da suka wuce a jimilce kamfanonin jiragen sama sun yi asara dala miliyan dubu 99, ta fannin karuwar kuɗin man petur, idan kuma al´amarin ya ci gaba, zai hadasa babbar illa.
A wani mataki na riga kafi, babban darakatan Fraport Dr Wilhelm Bender ya bayyana matakan da suka dauka:Yace don rage wannan asara mun ɓullo da wasu sabbabin ayyuka, wanda ba su shafi zirga zirga da jirage ba, sannan akwai taimakon juna ta fannin cuɗaya tsakanin filaye saukar jirage da kamfanoni jiragen sama, ta yadda zasu gama ƙarfi domin magance wannan matsala.
Burinmu shine kamin zuwa shekara ta 2020, mu karkata kashi 80 cikin ɗari na harakokinmu, a wasu sauran hada- hada wanda ba na jigilar mutane da kaya ba.
Bugu da ƙari,wani mataki da za mu ɗauka shine mu taƙaita zirga zirgar jirage zuwa yankunan da babu buƙƘata mai yawa.
A game da haka,zamu bada ƙarfi a yankuna kamar gabacin Turai, China Indiya, da wasu sassa na Latine Amurika.
Tunni dai ƙididiga ta gano cewar, kamfanoni jiragen sama 35 suka rufe a dalili da tsadar man petur, shine karo na farko a duniya da aka fuskanci irin wannan matsala.
Daga jerin matakan da Fraport ya ɗauka, akwai yarjeniya tare da wasu kamfanoni jiragen sama na duniya, kamar yadda Stefan Rüter baban jami´in dake kula da hulda da ketare ya bayyana:A halin yanzu mun ƙulla sabuwar mu´amila tare da filayen saukar jiragen sama na ƙasar Senegal da Masar a Nahiyar Afrika, sannan mun rattaba hannu akan yarjeniya da Saudi Arabiya a game da filayen saukar jiragen sama na Jidda da Ryad, tunni mun aika ƙurraru domin su koyar da ma´aikatan wannan kamfanoni husa´o´i na zamani.
Jami´an ya bada ƙarin haske a game ada nau´o´in wannan horo da suke baiwa mai´akatan kamfanoni jirgan sama da suke hulɗa tare da su:Da dama daga tashoshin saukar jiragen sama na buƙatar husa´o´i iri na zamani domin gudanar da ayyukan.
Muna koya masu wannan aiki , misali kaka ta kamata a tafiyar da haerakokin gudanarwa a tashar saukar jirage.
Fraport na da mu´mila da tashoshin jiragen sama 13 a duniya,ta hanyoyi guda biyu kamar jami´ain ya bayyana, wanda suka hada da saka jari da kuma horo: Hanyar farko itace zuba jari, wato muna zuba kuɗaɗe domin gudanar da hada hadar kasuwanci tare da filayen saukar jiragen sama, ribar da aka samu a raba daidai ruwa daidai tsaki, idan kuma asara akayi, itama a raba ta daidai ƙarfin hannen jarin ko wane ɓangare.
Sannan hanya ta biyu itace mu bada horo, ta la´akari da ƙurewa dake gare mu ta wannan fanni.
Wani batu da hukumomin Fraport suka duƙufa kan shi a halin yanzu, shine na faɗaɗa filin saukar jiragin, suna buƙatar kammala wannan aiki kamin shekara ta 2020.











