1. main content
  2. main navigation
  3. extra content
  4. head navigation
  5. search
  6. Choose form 30 Languages


 

Siyasa | 16.07.2008

Dangantakar Jamus da Aljeriya

Ziyarar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a ƙasar Aljeriya

Samun canjin al'amura shine abin da yake da muhimmanci a bangaren Jamus da kuma a bangaren kasar Algeria, musmaman idan aka yi batu na  dangantakar ciniki, wanda shine babban abin da ya hade kasashen biyu.

Katrin Laskowski,  shugaban sashen Afrika ta arewa a kungiyar hadinkai da kasashen Afrika ta Jamus tace:


Gas da man fetur sune yanzu  abubuwa biyu da suka fi daukar hankali ga kowa da kowa. Algeria ita ce kasa ta ukku a jerin wadanda suka fi  mallakar arzikin gas a duniya, kuma ana sane da cewar Jamus kasa ce dake da matukar bukatar gas din  domin amfanin ta na yau da kullum.


To sai dai Algeria baio kamata  ta maida hankaln ta gaba daya ga arzikin gas da man fetur kawai ba., ko da shike wadannan albarkatu biyu ne   suke baiwa kasar kashi hamsdin cikin dari na  kudaden ta gaba daya. Wajibi ne kasart ta bude kofofin ta ga wasu fannonin na tattalin arziki, idan har tana bukatar   nan gaba ta sami nasarar  rage matsalar rashin aikin yi a kasar. Ko da shike  Algeria tana sa ran  kudin da take samu  daga  gas da man fetur zai karu, amma  wadfata da al'ummar kasar suke  fatan zai samu daga   man da gas,  wata ci gaba rda zama mafgarki a garesu.


Sigfried Breuer,  wakilin   cibiyar  dangantakar tattalin arziki da kasashen ketare ta Jamus a yankin Maghreb, ya baioyana ra'ayin cewar   sauke tsohon Pirayim minista kasar ta Algeria da aka yi a watan Yuni, wata alama ce  ta bude kofofin kasar ga wasu fannonin na tattalin arziki.


Tsohon Pirayim minista Abdelaziz  Belkhadem ya kasance makusancin kungiyoyin musulmi ne masu tsattsauran ra'ayi, dake baiyana kyamar su ga tsarin tattalin arziki irin na kasashen yamma, saboda hjaka baya bada gudummuwar sa ga ci gaban  tattalin arzukin kasar ta wnanan fuska., duk da sanin cewar a Algeria  Pirayim minista bashi da wnai karfin iko. Shugaban kasa shine wuka, shine  nama a yanke  ko wane kudiri.


Abdelaziz Belkhadem ya rika mukamin Pirayim ministan Algeria tsawon shekaru biyu. A Tsakanin wnanan lokaci, an kasa samun   nasarar aiwatar da shirin da aka sanar na gyara ga tsarin tattalin arziki. Yanzu  kuwa  aiwatar da wnanan shiri  ya  tattara ne a  hannun  Ahmed Ouyahia, wanda  mai matsakaicin ra'ayi ne a fannin tattalin arziki. A game da   yan kasuwa da masu masana'antun Jamus, ko da shike zasu ci gaba da takara da   takwearforin su na Faransa, amma taken Made in Germany, wato darajar kayaiyakin da aka yi a Jamus yana da muhimmanci, kamar yadda Katrin Laskowski ta nunar.

Cibiyar  dangantakar ciniki da kasashen ketare ta Jamus tace yanzu haka kamfanonin kasar  kimanin dari da hamsin ne suke  aiyukan su a Algeria. Jamusawa ne suke aikin gina hanyoyin jirage na karkashin kasa a Algiers, uma Jamusawan ne suka karbi  masana'antun  yin sabulun wanki a kasar ta Algeria, kuma sune aka basu aikin gina daya dagha ciin masallatan da suka fi girma a duniya a can.


Katrin Laskowski tace kamfanoni da masana'antun na Jamus, da alamun babu  abin da ya dame su da  gaskiyar cewar ana keta hakkin yan Adam a kasar ta Algeria. Abin dake da muhimmanci shine, Jamusawan  wajibi ne su nemi  wata kafa ta  samun  gas, a kokarin su na rage dogaro da Rashqa. Algeria kuwa tana iya  cika burin na Jamus game da haka.

 

Umaru Aliyu

 
Share this article

Send us an e-mailSendPrint

More on the topic