Duniyar ɗan Adam | 30.07.2008
Sakamakon taron WTO
An watse baram baran a taron Ƙungiyar Cinikaya ta Duniya da ya wakana a birnin Geneva
Bayan kwanaki kussan goma na tattanawa a birnin Geneva, wakilan ƙasashe membobin Ƙungiyar cinikaya ta duniya sun watse baram baram ba tare da cimma burin da aka sa gaba ba.
Taron na Geneva ya ƙudurci cimma matsaya guda, tsakanin ƙasashe 153 membobin Ƙungiyar cinikaya ta duniya ,wato WTO kokuma OMC a game da batun daidaita sahun saye da sayarwa tsakanin ƙasashe dabam dabam na duniya.
To saidai bayan kwanaki kussan10 na mahaurori, an kasa cimma daidaito, dalili da matsayin da Amurika da Indiya suka ɗauka.
Shugaban Ƙungiyar cinikaya ta Duniya Pascal Lamy, ya bayyana matuƙar takaici a dangane da wannan ƙiƙi-ƙaƙa, ya kuma buƙaci a cigaba da tuntuɓar juna, har sai an kai ga tudun dafawa:
Muna buƙatar fuskantar wannan ƙalubale, lalle a halin yanzu abun na da kamar wuya, to ama duk da haka ya zama wajibi ga membobin WTO sun cimma matakin warware wannan matsala cikin fahintar juna.
Pascal ya san da cewar akwai zabuka tafe a kaasshe Amuruika da Indiya ƙasashe biyu da suka hana ruwea gudu a cikin wannan tattanawa, saboda haka, babu mamaki ,cenji sabin magabata ya haifar da sauyin alƙiblar ƙasashen biyu a game da manufofinsu a Ƙungiyar cinikiya ta duniya.
kamar yadda ta wakana baya, a wannan karo ma batun harakokin noma suka dabaibaiye mahaurorin.
Amurika ta yi tsaye kan bakanta na bada tallafi fiye da ƙima ga monomanta, abunda ke nakasa kasuwancin albarkatun noma a ƙasashe masu tasowa.
A nata ɓangare ƙasar Indiya ta yi tsawuwar gwamen jaki a game da batun gita shingen cinikaya a iyakokinta, mussamman ta fannin hana shiga kokuma fitar da wasu kaya.
wakiliyar Amurika a taron Susan Schwab, ta yi Allah wadai ga wannan mataki:Ta la´akari da yadda farashen kayan masarufi suka yi tashin gwabran zabi a cikin kasuwanin, abun takaici ne, wasu ƙasashe su cigaba da gitta shingen cinikaya akan iyakokinsu.
A nasa gefe komishinan Ƙungiyar taraya Turai mai kula da harakokin ciniki Peter Mandelson, ya rataya lefin wannan koma baya ga dukan ƙasashe membobin WTO ba tare da bambanci ba: Mu duka muna da hannu a cikin wannan kasawa, saidai illolin da za su biyo baya, za su bambanta daga wannan ƙasa zuwa wace, mussamman ƙasashe masu tasowa zasu fi fuskantar matsaloli.
A halin da ake ciki dai ƙasashe na cigaba da hurta albarkacin bakin su a game da sakamakon taron na birnin Geneva.
Ministan harakokin wajen Brazil, ya bayyana matuƙar ɓacin rai a dangane da kwan gaba kwan baya, da ake yi a mahaurorin WTO wanda suka ka jiɓanci cinikiya, ya ce wannan al´amari, ba ƙaramar asara ce ba ga dukkan ƙasashen duniya.
Itakuwa wakilioyar kasar France ta bayxyana mahimanci samun fahintar juna, tsakanin ƙasashen Ƙungiyar Tarayya Turai, domin a cewar ta, akwai saɓanin ra´ayoyi tsakanin su ,a game da wasu batutuwa da suka shafi wannan tattanawa.














