1. main content
  2. main navigation
  3. extra content
  4. head navigation
  5. search
  6. Choose form 30 Languages



 

 | 13.05.2008 | 14:00 UTC

Taron ministocin tattalin arziƙin Afirka a Mozabique

Ministoc tattalin arziƙi daga duk faɗin Afirka za su hallara a ƙasar Mozambique a gobe laraba don gudanar da taron shekara shekara na bankin ci gaban Afirka a daidadi lokacin da ake yi wa nahiyar hannunka mai sanda a game da hauhawar farashin kayan avbinci da man fetur. Ana sa rai ministocin tattalin aeziki da dama da shugabannin manyan bankuna na daga cikin wakilai dubu da dari biyar da za su halarci taron na kwanaki biyu a Maputo babban birnin Mozambique. A cikin wani rahoto bankin ci gaban Afirka yayi kashedi cewa  karin da ya ninka parashin kayan abinci da Afirka ke dogaro akansu a watannin da suka gabata zai iya jefa nahiyar a cikin wani hali na tsaka mai wuya.