| 13.05.2008 | 14:00 UTC
Tsamin dangantaka tsakanin Sudan da Chadi
Kasar Chadi ta rufe dukan iyakokinta da Sudan ta kuma katse hulɗar tattalin arziƙi da ita bisa zargen da ta yi mata cewa tana da hannu a cikin harin da 'yan tawaye suka aiwatar kusa da Khartoum. Wani wakilin Chadi ya zargi Sudan da neman hanzarin kai wa Chadi hari. A ranar lahadin da ta ta gabata ne Sudan ta yanke duk wata huldar diplomasiya da Chadi tana mai zargenta da tallafa wa 'yan tawaye a lardin Darfur. Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch ta nuna damuwarta a game da yadda ake kamen kai mai uwa da wabi a birnin Khartoum bayan harin da 'yan tawaye suka kai kusa da babban birnin. Ƙungiyar tace ta samu rahotann dake nuni ga cewa ' yan tawayen suna azabtar da mutane kuma sun yi wa aƙalla mutane biyu kisa. Tace kamata yayi dakarun gwamnatin Sudan da 'yan tawayen baki ɗayansu su yi aiki da dokokin yaƙi don kada su gallaza wa farar hula.





