| 13.05.2008 | 14:00 UTC
Israila za ta sassuta takukumin da ta ƙaƙaba wa Falisdinu
Wakilin Ƙungiyar Tarayyar Turai a Gabas ta Tsakiya wato Tony Blair yace Israila ta yarda da sassauta takunkumin hana tafiya da ta ƙaƙaba wa Falisdinawa a Gaɓar Yamma da Ƙogin Jordan. Blair ya ba da sanarwar haka ana saura kwana ɗaya shugaba George Bush ya kai ziyara a wannan yanki ne domin bunƙasa tafarkin tattaunawa tsakanin Israila da Falisdinu. Sai dai kuma wani kakakin sojin Israila ya nunar da cewa za a gudanar da canje canjen da za a yi ne nan gaba kuma da sharaɗin cewa ba zasu kawo cikas ga tsaron Israila ba. Blair ya sanar cewa Israila za ta fid da wani shinge da ta sa kusa da birnin Hebron dake Gaɓar Yamma da Ƙogin Jordan a wannnan mako.





