| 04.07.2008 | 14:00 UTC
Siyasar Zimbabwe
Ƙungiyar tarayyar Turai ta yi kiran sake gudanar da sabon zaɓe a Zimbabwe bayan aiyana kan sa a matsayin shugaban ƙasa da Robert Mugabe yayi, a zaɓen da shi kaɗai ya tsara takara a watan da ya gabata wanda duniya ta yi tur da Allah wadai da shi. Ƙungiyar tarayyar Turan mai wakilan ƙasashe 27 ta ce mafita ta samun masalaha a rikicin na Zimbabwe shine sake tuntuɓar alúmar ƙasar ta hanyar sahihin zaɓe na dimokraɗiya ba tare da wani jinkiri ba. Ita ma ƙasar Botswana wadda ke makwabtaka da Zimbabwe, a ta bakin Ministan harkokin wajen ta Phandu Skelemani ta yi kira ga ƙungiyar raya cigaban ƙasashen kudancin Afirka SADC da cewa kaɗa ta amince da sake zaɓar Mugabe a matsayin shugaban ƙasa. A waje guda dai Mugabe ya faɗa a yau cewa zai amince da shawarwarin kawo ƙarshen rikicin siyasar ne kawai idan aka amince da shi a matsayin shugaban ƙasar. Mugabe ya shaidawa manema labarai a birnin Harare bayan dawowa daga taron ƙungiyar gamaiyar Afirka da aka gudanar a ƙasar Masar cewa labudda shine shugaba da alúmar Zimbabwe suka zaɓa yana mai cewa kada ma yan adawa su yi tunanin ko zai sauya shawara kan matsayin sa. Dubban jamaá ne suka yi dafifi domin yi masa maraba a yau jumaá bayan dawowa daga taron na Sharm el-Sheikh.




