1. main content
  2. main navigation
  3. extra content
  4. head navigation
  5. search
  6. Choose form 30 Languages



 

 | 23.07.2008 | 19:00 UTC

Iran tace ba zata bada kai bori ya hau ba.

Shugaban ƙasar Iran Mahmoud Ahmedinejad ya lashi takobin cewa Iran ba zata bada kai bori ya hau ba a game da taƙaddamar shirin ta na Nukiliya. Ahmedinejad ya shaidawa taron jamaá a kudu maso yammacin ƙasar cewa alumar Iran na nan akan bakan su ba kuma za su ja da baya ba akan ƙudirin su don matsin lambar manyan ƙasashen duniya ba. Wannan jawabi nasa ya zo ne bayan da manyan ƙasashen na duniya makwanni biyu da suka wuce suka gargaɗi Iran ta amsa tayi na baya bayan nan da suka yi mata ta kawo ƙarshen taƙaddamar Nukiliyar wanda aka kwashe shekaru biyar ana ta cece-kuce akan sa da kuma ya haifar da fargabar tashin hankali a yankin dama kuma haddasa tashin gwauron zabi na farashin mai a kasuwannin duniya. Fadar gwamnatin Amirka tace har yanzu tana da Imanin cewa Iran zata yi watsi da shirin Nukiliyar domin idan ba haka ba takunkumin gamaiyar ƙasa da ƙasa za su biyo baya.

Taron ƙungiyar ciniki ta Duniya

Wakilan ƙungiyar ciniki ta duniya WTO na ƙoƙarin cimma yarjejeniya kan kwaskwarima ga manufofin cinikayya ta duniya. Ministocin na fatan cimma matsaya game da batutuwa da suka shafi harkokin noma da kayayyakin masanaántu. Ministan ciniki na ƙasar India Kamal Nath yayi maraba da sauyin matsayi da Amirka ta ɗauka game da sassaucin da take yiwa manoman ta. A jiya Talata Amirka ta yi alƙawarin taƙaita rangwamen da take baiwa manoman ta izuwa ƙasa da dala biliyan goma sha biyar, Amirkan kan baiwa manomanta tallafin dala biliyan goma sha bakwai a kowace shekara. Batun sassauci da manyan ƙasashe ke baiwa manoman su na cigaba da ɗaukar hankali a wajen taron na bana.

Angola ta buƙaci ɗage takunkumi akan Zimbabwe

Ƙasar Angola ta yi kira ga ƙungiyar tarayyar Turai ta gaggauta ɗage takunkumin da ta sanyawa shugabanin Zimbabwe, tana mai cewa hakan zai haifar da naƙasu ga shawarwarin da ake na sulhunta rikicin siyasar ƙasar. Ministan harkokin wajen Angola Joao Miranda wanda ya yi wannan kiran yace babu wani dalili da zai hujjanta wannan mataki na cigaba da ƙaƙabawa shugabanin Zimbabwen takunkumi. A saboda haka yace wajibi ne a cire dukkan wani tarnaƙi da zai kassara shawarwarin. kalaman na Miranda sun zo ne kwana guda bayan da Ministocin harkokin wajen ƙungiyar tarayyar Turai suka faɗaɗa takunkumi akan Zimbabwe duk da cimma yarjejeniyar da aka yi tsakanin shugaba Robert Mugabe da madugun adawa Morgan Tsvangirai kan yadda za su gudanar da shawarwarin rabon madafan iko don kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa. Takunkumin hana zurga-zurga da riƙe kadarorin wanda aka sanyawa Mugabe da manyan muƙarraban sa tun shekarar 2002 a yanzu an ƙara faɗaɗa ta inda ta kunshi manyan jamián ƙasar su 168 da kuma wasu kamfanoni guda Huɗu.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Somalia yayi kiran huta masu laifi

Manzon musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya a Somalia Ahmadou Ould Abdallah ya gargaɗi waɗanda suka aikata laifukan keta haddin bil Adama da cewa basu da wurin buya, yace wajibi ne su fuskanci shariá. Ahmadou Ould Abdallah ya shaidawa manema labarai cewa wajibi ne a gurfanar da dadukkan  waɗanda suka aikata taása ta kisan bayin Allah waɗanda basu ji ba su gani ba. Abdallah wanda ya gabatar da jawabi ga kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya yace ya kamata mutane waɗanda suka ɗauki tsawon shekaru suna aikata ba daidai ba su sani cewa watan wata rana dole ne su girbi abin da suka shuka. Yana mai cewa cafke tsohon jagoran Sabiyawan Bosnia Radovan Karadzic da aka yi kwananan bisa laifukan yaƙi ya isa misali ga waɗanda suka aikata laifukan yaƙi a Somalia su san cewa basu da wurin buya a ko ina. Ould Abdallah ya kuma jaddada buƙatar tura dakarun kiyaye zaman lafiya na ƙasa da ƙasa zuwa Somalia domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro da sasanta alúmomi da kuma taimakawa wajen rabon kayayyakin agaji ga jamaá.

Kotu ta wanke Mousa Kaka daga zargin da ake masa

Wani babban mai shariá a jamhuriyar Niger ya kori ƙarar dake tuhumar wani ɗan jaridan gidan Radion RFI Mousa Kaka wanda aka tsare har tsawon watanni goma bisa zargin cewa yana haɗa kai da yan tawayen Abzunawa. Wannan dai shine karo na biyu da Alƙalai ke fatali da ƙarar tare da bada umarnin sakin ɗan jaridar. Mousa Kaka wanda har ila yau shine Daraktan wani gidan Radio mai zaman kan sa a ƙasar Niger, an kuma tuhume da shi da yiwa gwamnatin maƙarƙashiya da cin manar ƙasa. Lauyan sa Mousa Koulibali ya shaidawa yan jarida cewa babban Jojin ya shaidawa wanda yake karewa cewa an kori ƙarar da ake tuhumar sa akan sa.