Tsadar man Fetur a duniya

Tsadar man fetur ta hadasa illoli masu yawa ga tattalin arzikin duniya.
Ɗaya daga cikin mahimman batutuwan da suka ɗauki hankalin jama´a a shekara bana, ta fannin tattalin arziki, shine tashin farashen man petur a kasuwanin duniya.
Ta la´akari da yadda amfani da man futur ya zama cilas a harakokin dabam dabam na rayuwarmu ta yau da kullum, wannan al´amari ya jawo cenje cenje masu yawa a tsarin rayuwar jama´a.
A matsayin waiwaiye adon tafiya, shirin zai maku bitar farashen man petur daga shekara ta 1970 zuwa yanzu.
A shekara ta 1970 wato shekaru 38 baya, an sayi gangar ɗanyan mai ɗaya, akan farashen dalla Amurika ɗaya kacal da centi talatin.
Bayan shekaru huɗu, ƙasashen Ƙungiyar da suka mallaki man petur wato Opec ,ta ƙara farashe zuwa dalla goma, a matsayin martani da yaƙin Kippour,da ya haɗa dakarun ƙasashen larabawa da na Isra´ila, wanda suka samu tallafi daga Amurika.
A shekara ta 1979 Iran ta ƙaddamar da juyin juya hali, kasancewar ta ɗaya daga ƙasashen da suka mallaki man Fetur, nan take !!! farashen ya tsula zuwa dalla 20.
A shekara ta 1980, yaƙi ya ɓarke tsakanin Iran da Irak, daga nan farashen gangar ɗayan mai ɗaya ta cigaba da hauhawa zuwa dalla kussan 40.
Jim kaɗan kamin yakin Golf a shekara ta 1990 farashen ya wuce dalla 40.
A watan Ogust na shekara ta 2005 mahaukaciyar guguwar Katrina ta hadasa ta´adi ga yankunan Golfe of Mexique dake ƙunshe da man Fetur.
A sakamakon hakan, gangar ɗanyan mai ɗaya a karon farko ta kai dalla 70.
Tafiya zuwa tafiya, a watan Janairu da ya wuce, gangar ɗanyan mai ta habra dalla 100.
A halin da ake ciki ,ta wuce dalla 130, kuma masana harakokin tattalin arziki sun yi hasashen cewar zata kai ga dalla 200 kafin ƙarshen wannan shekara.
Allah kyauta,Hausawa kance wai mutuwar wani tashin wani a yayin da mafi yawan ƙasashen duniya ke kuka da hawaye a game da tsadar man petur, sukuwa ƙasashe da suka mallake shi, gaba ta kai su gobara titi, domin suna samun rarar kuɗaɗe ta fitar hankali.
Daga cikin ƙasashen dake kan gaba, a jerin ƙasashen da suka fi samun kuɗi daga man furtur sune ƙasashen yankin Golf.
A shekara da ta gabata, wannan ƙasashe sun samarwa kansu kuɗi misali dalla miliyan dubu ɗari huɗu da bakwai daga cinikin man fetur da iskan gaz.
Sannan hasashen da suka gudanar ya gano cewar, idan har farashin mai ya tsaya kan dalla Amurika 100 ko wace ganga ɗaya, wannan ƙasashe ya zuwa shekara ta 2020, za su samu rarar kuɗi da ta kai dalla miliyan dubu har sau dubu tara daga cinikin man Fetur.
Juya wannan kuɗi ya zama jari,, ya zama babban ƙalubale ga ƙasashe yankin Golf, domin a halin yanzu sun yi sanhi da zuba jari a ƙasar Amurika, kamar yadda Frauke Heard- Bey masaniyar tarihi da tayi shekarau 40 a Abu Dhabi ta nunar:
A yanzu ƙasashen yankin Golf basu matsa lambar cewar lallai sai sun zuba jari a Amurika,
A cen baya sun yi hakan amma a yanzu wanda ma ke da jarin a Amurika sukan kwashe shi su zuba a wani wuri na dabam.
A shekarun farko ƙasashen yankin Golf sunyi amfani da kuɗaɗen su na cinikayar man fetur, domin gina makarantu asibitoci da sauran ayyuka na jin daɗin rayuwar jama´a.
A jimilce, ƙiddidigar ta gano cewar, ƙasashen yankin Golf, su shida, sun kashe magudan kuɗaɗe wuri na gugar wuri, har dalla miliyan dubu har sau dubu ɗaya da ɗari tara don kyauttata rayuwar jama´a.
A halin da ake ciki rayuwar wannan ƙasashe ta kai matsayin ta ƙasashen turai, saboda haka sun daina gine- ginen makarantu da asibitoci, sun fi buƙatar zuba jari a bankunan ko a cikin hada hadar gidaje,da ta kamfanoni da masana´antu.
Burin da suke buƙatar cimma shine, ƙarfafa cigaban ƙasa ba tare da yin dogaro da man petur ba, ta la´akari da cewar ko badaɗe ko ba jimma, rijiyoyin mai za su ƙwahewa.
Saɓanin ƙasashen yankin Golf, a Tarayya Nigeria, ɗaya daga ƙasashen da suka mallaki albarkatun man petur, jama´a ba ta gani ba a ƙass,duk da ɗimbin kuɗaɗen da ƙasar ke samu a hada hadar kasuwancin man petur da duniya, har yanzu jama´a na fama cikin matsaloli dabam dabam, kamar yadda Al haji Ahmed Mohamed Makarfi tsofan gwamna Jihar Kaduna buga da ƙari, shugaban komitin kuɗi a Majalisar Tarayya ya bayyana.
Al Ahmad Maƙarfi ya yaba matakin da shugaban ƙasa Umaru Musa ´Yar Aduwa ya ɗauka na ware dalla miliyan dubu daga albarkatun man petur, domin magance mastalolin wutar lantarki da suka zama gagarabadau a Nigeria,sannan ya shawarci ɓangarorin dake da ruwa da tsaki a tafiyar da harakokin mulkin Nigeria su sake saban shiri, ta yadda al´ummar za ta ci gajiya kuɗin da ƙasar ke samu ta hanyar cinikin man petur.
Ƙasashe da Ƙungiyoyin dabam dabam na duniya suns higa tunanin abubuwan dake hadasa hauhauwar farashen mai a duniya da kuma hanyoyin warware wannan matsala.
A yayin da yake hurtuci a kai batun Dora Borbeley masani ta fannin makamashi ya bayyana dalilai kamar haka:
Buƙatar mai ta ƙaru matuƙa, daga ƙasashe masu tasowa, da wasu masu ƙarfin tattalin arziki kamar Japan da ƙasashen turai masu amfani da Euro.
Amurika ce kaɗai ba ta bayyana bukatar ƙarin mai ba.
Wasu daga jerin matsalolin da suka jawo matsalar hauhawan farashen man sun haɗa da kariyar darajar dalla Amurika da kuma tashe tashen hankulla da ke wakana a yankin Niger Delta na Taraya Nigeria, wanda a sakamakonsa kamfanoni haƙar mai suka rage yawan man da suke haƙowa.
Yahouza, Sadissou | www.dw-world.de | © Deutsche Welle.